WASHINGTON, DC —
A lokacin da yake jawabi a gaban gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno da Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu, mahaifin wata dalibar da aka sace daga makarantar sakabdare ta Chibok yace a lokacin da suka ji labari, sun garzaya makarantar domin su san abinda ke faruwa.
Daga nan sun yi kwamba suka dauki babura kamar guda 150, wasu dauke da mutane har 3, suka abka cikin daji neman 'ya'yansu. Yace sun tarar da wasu gidaje kwaya biyu cikin daji da mata masu yawa, kuma da suka yi gaba, sun ji labarin cewa an ga 'ya'yansu, su na nan kusa a cikin wani daji, amma an gargade su cewa muddin suka shiga, ba zasu fito da rai ba.
Ga cikakken bayanin da wannan mutumi yayi...

Your browser doesn’t support HTML5