Na Farko a Tarihin Italiya da aka Jagoranci kungiyoyi Dabam-Dabam Zuwa ga Lashe Gasar Lig-Lig

Massimiliano Allegri ya zamo mai koyar da wasa na farko a tarihin Italiya, da ya jagoranci kungiyoyi dabam-dabam guda biyu zuwa ga lashe gasar lig-lig ta Italiya, Serie A, a shekararsa ta farko da karbar ragamar wadannan kungiyoyi, a bayan da Juventus ta doke Sampdoria ta zamo zakarar lig ta Italiya.

Shekaru 4 a bayan da ya yi irin wannan bajimta a kungiyar AC Milan, a 2011, Allegri ya sake lashe wani kambin da Juventus wadda ta kanainaye tamaula a kasar Italiya tun bayan gwanintar da AC Milan din ta yi a can baya

Gobe talata, zai fuskanci kalubalensa mafi girma ya zuwa yanzu, inda zai jagoranci Juventus a karawar da zata yi da Real Madrid a zagayen fariko na wasan kusa da karshe na cin kofin zakarun kulob na Turai. Koda yaya wasan na gobe zai kasance, nasarorin da Allegri ya samu a bana sune mafi yawa da tasiri ya zuwa yanzu a matsayinsa na kwach.

Tuni ma masana tamaula suka ce irin bajimtar da ya nuna a zaman kwach, ya zarce bajimtar da ya nuna lokacin da yake dan wasa, inda ya buga kwallo ma kungiyoyi har 11, amma bai yi fice sosai ba.