Nyako yace Zasu Je Gaban Kotun Duniya, Sheikh Bala Lau Yace Obasanjo Ya Fadi Gaskiya - 21/4/2014

Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa, yace su na tattara bayanan da zasu ba su sukunin gurfanar da gwamnatin Najeriya a gaban kotun duniya bisa tuhumar kisan kare dangi ma ‘yan arewa. Gwamna Nyako yayi zargin ana sanya sojoji su na kashe ‘yan’uwansu sojoji.

Shi ma shugaban kungiyar izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah, Sheikh Bala Lau, yace lallai akwai kamshin gaskiya a cikin bayanan da tsohon shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo, yayi kwanakin baya.

Gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta musanta wannan zargin.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya A Takaice Yau Litinin - Nyako yace Zasu Je Gaban Kotun Duniya - 1'30"