Ranar Juma’a NFF Zata Tabbatar Da Stephen Keshi

Coach Stephen Keshi speaks to members of the Super Eagles at practice in Abuja before their World Cup qualifier against Ethiopia.

Ana kyautata tsammanin hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, zata tabbatar da Stephen Keshi a matsayin Koch ‘din Super Eagles ranar Juma’a.

Sakataren hukumar kwallon dakta Sanusi Mohammed ya bayyana cewa za’a sanar da wanda zai jagoranci kungiyar Super Eagles a karshen makon nan.

Ata bakin sa yace, “na yi muku alkawarin zuwa Juma’a, batun wanene Koch ‘din Super Eagles zai zamanto tarihi saboda za’a fitar da kowaye. Don haka ranar Juma’a dukkan mu zamu san sabon Koch ‘din Super Eagles.”

Ana tsammanin Keshi zai taso daga Benin zuwa Abuja, a yau Alhamis dai dai da lokacin da za’a fitar da sanarwar nadin nasa.

Wata majiya ‘karfi ta gayawa mujallar Goal, cewa Keshi ya amince da shugabannin hukumar kwallon kan sabon kwanturagi na shekara biyu wanda zai kare bayan wasan cin kofin nahiyar Afirka, idan har Najeriyar ta sami nasarar shiga wasan.

Sabon kwantiragin dai zai kai Stepen Keshi ga ‘daukar albashin Naira Miliyan biyar a wata.