Raya su Tafkar Raya Al’uma ne

Mata

Majalisar Dinkin Duniya, ta ware 8, ga watan Maris na kowace shekara, a matsayin ranar bukin Matan Duniya, taken bukmin mata na wannan shekarar shine “Karfafa mata karfafa al’uma”.

A bukin na bana a jihar Gombe, Gwamnan jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya baiwa mata tallafin kudi domin karfafasu kamar taken na bana. Ya kara da cewa raya mata tafkar raya al’uma ne.

Wasu daga cikin matan da suka anfana da tallafin da Gwamnan ya bada sun nuna matuar farin ciki, wasu kuma suka ce tabbaci hakika tallafin zai inganta rayuwarsu.

Kwamishinar mata , ta jihar Gombe Hajiya, Sa’adatu Mustapha Ali, tayi bayani kan irin mukamai da mata ke rike dasu a jihar Gombe, Kama daga Kwamishinoni, daraktoci da kuma dawwamammun sakatarori.