Facebook na aikin kirkirar wata sabuwar manhajar kallon hotan bidiyo wadda akafi sani da App wato Apliction a turance, ita dai wannan App za’a kirkireta ne yadda zata baiwa mai kallon hotan bidiyo ko daukar hotan bidiyon damar kallon duk abinda ke kewayansa, wato gaba da baya, gefe da gefe.
Wannan kuwa dama ce da aka baiwa masu amfani da shafin sadarwa na Facebook, ta inda mutane masu kallon hotunan bidiyo su zabi bangaren da suke son kallo ta hanyar juya wayar su, ba tare da juya na’urar ‘daukan hotan ba.
Kamar yadda bayanai ke nuni ita dai wannan App zatayi aiki a duk fitattun manhajar wayoyin zamani, wanda suka hada da Android da ios wato Apple. A yanzu haka dai kamfanin na Facebook ya biya dala biliyan biyu ga kamafanin Oculus rift, domin fara aikin wannan App, inda ake tsammanin kammalawa cikin shekara mai zuwa.
A yanzu haka dai akwai na’urar ‘daukan irin wannan hotan bidiyo da ake kira 360 degree video, duk da yake dai ba kowa bane yasan da ita ba ko ya mallake ta ba, sai wane da wane a saboda tsadar da take da ita. Duk wanda ke da sha’awar ganewa idon sa yadda yadda wannan fasaha take, to zai iya ziyartar shafin www.youtube.com ya rubuta 360 degree bidiyo domin kallon abin mamaki, kafin ta zo ga masu amfani da shafin Facebook.