‘Yan sandan birnin Sarasota jihar Florida dake Amurka, sunce sun kama wani matashin daya shiga gidan wata mata ya kuma kishingide barci akan babbar kujerar ‘dakin hutu na gidan.
An kame matashin mai suna Timothy Bontrager mai shekaru ashirin da tara da haihuwa da safiyar Asabar.
Jami’an tsaro sun bayyana cewa masu gidan sun farka da sanyin safiya inda suka sami Bontrager kwance kan kujera yana barci. Sai matar gidan ta tashe shi tana tambayar sa me yake yi a gidan ta? Ya dai bata hakuri ya kuma fice alokacin da take cewa zata kira ‘yan sanda.
Masu gidan sun gayawa jami’ai cewa Bontrager ya shiga gidan ne ta wata taga da ba’a kulle ba dake bayan gidan. Daga bayane suka farga cewa jakar ajiye kudin su ta bace wadda ke kunshe da lisin din tuki da katin cire kudi a banki da sauran wasu kayayyaki masu muhimmanci duk sun bace.
Ba tare da bata lokaci ba ‘yan sanda dai suka kame matashin, har yanzu dai babu wani bayani kan ko matashin yana da lauya mai kare shi.