Shawarar Al’amin Da Wasila Kan Auren ‘Yan Matan Fim

Mawakiya, kuma jarumar fina-finan Hausa, Sakna Gadaz

A cikin duniyar masu yin fina finai na wannan zamani, dayawa muna gani gurin masu yin wannan sana’a musammam ma mata, cewa da zarar sunyi aure ba tare da an dade ba sai muji auren ya mutu, tambayar da muka yiwa wasu ma’aurata kuma wadanda sukayi sana’ar fina finai Al’amin Chiroma da matar sa Wasila Isma’il.

Game da dalilan dake jawo rashin karko tsakanin masu yin fina finai ko ‘yan wasan Hausa, a cewar Al’amin Chiroma, shidai aure wani abune da Allah ya sanya shi ya zama al’ada a cikin halittu daga mutane har ma da dabbobi, aure dai shine ginshikin rayuwar ‘dan Adam, ana kuma samun matsala idan namiji ya auri mace kuma ya daina kallon ta a matsayin abokiyar zama, ya rika kallon ta a matsayin ta ko aikin ta missali kamar ace ‘yar kasuwace, babbar ‘yar siyasace da dai sauransu, to idan miji ya kalli matarsa ta irin wanan hanya to har kullum zai rika hukun tatane a matsayin haka ‘din.

Al’amin dai ya bada missali akan aurensu inda yace kamar yadda ya auri Wasila, ita dai ‘yar wasan fim ce kuma idan har ya fara kallon ta da wannan fuskar to tabbas zasu fara samun wasu abubuwa suna ta sake sake, to amma idan akace ana duba aure kasancewar ibada ne, kuma ana ibadane ba tare da san rai ba.

Ita kuma Wasila, tace abinda ta sani kan jigon aure shine ayi don Allah, kuma a hada da hakuri a fuskanci juna da kai zuciya nesa, ta kuma ce yin aure ana so mace ta auri abokinta ba masoyiba, idan kuma tasamu biyun a hade to yana da kyau, domin aboki dashi ake shawara.