Ni Na Fara Sanyawa A Fina-Finan Hausa In Ji Shu'aibu Lilisco

Shuaibu Idris Lalisco

Yau Dandalin Voa ya karbi bakuncin Shuaibu Idris, jarumi kuma producer, wanda ya shafe shekaru ashirin da biyar yana harkar fina finai kuma ya kasance mutun na farko da ya fara sa waka a fim din sa.

Yace “nayi aiki a hukumar tarihi da aladun gargajiya wanda ta kai matsayin a wanna lokacin ina cikin fitattunm’yan wasan da ake ji dasu a hukumar tarihi da aladun gargajiya, na je irinsu Amurka, Libya, Venezuela da Ethiopia, duk a harkar nishadarwa.”

Ya kara da cewa “A lokaci da harkar fim ta fara shigo fim din nan a farko dana fara sa hannu a kai shine Kulba na barna wanda muka yi shi a Bauchi naje as crew bayan na dawo 1996, muka fara shirya wani fim mai suna “Dashen da Allah keso” da Sani Musa mai iska, wanna shine fim na farko wanda na fara sa masa rawa a ciki ganin wannan rawar da nayi sai ta ja hankalin wanda suka fara shirya fina finai sai sarauniya fim production suka kira ni suka bani damar in shirya masu raye rayen da za’a ayi a fim din Sangaya Sa’a tafi gata nayi ‘yar Gudille, nayi taskar rayuwa nazo nayi fim di na mai suna salsala.”

Mafi yawan mutane zuna korafin cewa wannan waka da ake sawa a fina finai ba aladar mu bace?

Baza a ce bamu da alada ta Waka ba ita kanta wakar ai akwai wace idan aka sa ta akan sata a hurumin da ta dace wani kuma ana dubawa aga yaya karfin labarin yake abun na tausayi ne ana so kuma a nishadatar da mutane sai a sako wannan wakar.

A fanin tsegumi kuwa daraktoci da sauran masuruwa da tsaki a harkar fina finan Hausa suka gana da hukumar tace fina finai na jahar Kano dake Najeriya, wata sanarwa ta ce an gayyaci daraktocin ne daga jahohin Kano da Kaduna da garin Jos da Katsina da Sokoto da Abuja domin su halarci taron da fatan an tattauna muhimman batutuwa.