Shirin Bana-Bakwai

A shirinmu na bana bakwai a yau mun leka majalisar wawsu matasa inda muka ji sabbin kalaman da suke amfani da su a junansu.

Idan ana maganar wani sai a ce kai gayen nan ya tanema’ana ya gane hirar da ake yi idan ka ce zan tabo ka a ta kurmarka ana nufin mutumin da ake hirar sa ba mai gane batu bane

Ko idan ana hira sai aka ce wannan gabine wato baya gane abin da ake fada ko ace akwai marayi a wajenka ma’ana ko da mota hanun wanda ake tambaya

Idan kuwa budurwa aka hango za’a cewa mutumin na fada da wannan yarinyar ma’ana shine ta cancanci yabo.

Idan kuma ka ce wa abokin ka kinko ya rungume ni wato anan ana nufin an fada kwata ko ana fatara ta rashin kudi.