Shirin Rabon Abincin Shan Ruwa A Jihar Kano

Dandalin VOA, ya sake waiwayan aikin rabon abinci na watan ramadana, domin jin ta bakin jama’a kan yadda wannan shiri yake tafiya, Wakiliyar Dandali Baraka Bashir, ta zaga wasu daga cikin cibiyoyin da ake ba da wannan abincin domin jin ta baki wasu daga cikin mutanen mazauna yankunan.

Mafi yawan alumma na korafin rashin tsari na yadda ake raba abincin, tare da rage hannu na adadin abinci da ake rabarwa sabanin yadda aka sa ba yi a baya.

Kan wannan korafi ne Dandali ya samu zantawa da Kwamishinan yada labarai Kwamarad Mohammad Garba, inda yace gwamnatin jihar Kano bata ce ta fito da tsarin tallafin da zai ciyar da duk al’ummar Kano ba, haka kuma yace wannan wani tallafi ne na dai dai gwarwado domin taimakawa masu bukata.

Mutanen dai na fatan za a gyara tsarin rabon abincin domin ya isa hannuwan mutanen dake da bukata.