WASHINGTON, DC —
Wani sojan Najeriya, yayi zargin cewa babu gaskiya a ikirarin da hukumomin tsaron Najeriya keyi cewa su na yaki da Boko Haram, domin kuwa, sun ga wadanda suka koyar da su yadda ake yakar ta'addanci su na taya 'yan Boko Haram fada.
Haka kuma sojan yayi zargin cewa akwai wani kwamandan sojoji a Bama, wanda ya kirawo su daga wani garin domin dafa ma sojojinsa baya, amma da suka shiga daji, shi sai ya janye sojojinsa da tankokin yakinsu da motoci masu sulke, ya bar su da kananan bindigogi kawai su na fuskantar 'yan ta'adda a cikin daji.
VOA Hausa ya shafe kwanaki 3 yana neman martani daga bakin jami'an tsaron Najeriya ko ma'aikatar tsaron kasar, amma babu wanda yace uffan.
Idan mun samu martanin hukumomin Najeriya kan wannan zargin, zamu kawo muku.
Ga kadan daga cikin abinda wannan soja yake fada...

Your browser doesn’t support HTML5