Ta Sayar Da Jikan Ta Dan Ta Sayi Babur

Jami'an tsaron 'yan sandan jahar Abiya, reshen Ngwa dake karamar hukumar Obingwa, sun kama wata mata da ba'a fadi sunan ta ba da laifin sayarwa da wani da ake zargin matsafi ne jikan ta mai shekaru uku da haihuwa.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, mai magana da yawun 'yan sandan jahar DSP Udeviotu Onyeke, ya bayyana cewa a yanzu haka matar na hannun jami'an tsaro, kuma ana ci gaba da bincike.

Onyeka ya kara da cewa, matar ta bar kauyen tare da jikan nata, bayan sati guda ta dawo inda tayi ikirarin bacewar yaron.

Shaidu daga kauyen sun bayyana cewa a lokacin da aka tambaye ta a game da yaron, nan take jikinta ya vkama rawar nuna rashin gaskiya, lamarin da yasa jama'r kauyen suka sanar da jami'an tsaron ba tare da bata lokaci ba.

Matar da ake zargin dai ta fada wa 'yan sandan cewar ta sayar wa da wani Boka da ba'a fadi sunan sa ba a Akwa Ibom jikan nata ne a kan kudi naira dubu dari, saboda tana tunanin tara kudinne domin sayen babur!

Da farko dai matar ta fara fadawa jami'an tsaron cewa ta baro jikan nata a wurin 'yar uwarta dake garin Aba ne, kafin da bincike yayi bincike ta fara bfadar gaskiya.

Mai magana da yawun jami'an ya bada tabbacin cewa zasu bi diddgin lamarin har sai sun gano inda yaron yake.