Kamfanin Facebook ya hada kai da wani takwaran aikin sa na Faransa mai samar da tauraron dan Adam da ake kira Eutelsat, domin harba wata na’ura a sararin samaniya wacce za ta taimakawa kasashen dake yamma da hamada shiga yanar gizo ko kuma internet kyauta.
Za’a kaddamar da wannan shiri ne a zangon watanni shida na karshen shekarar 2016.
Ana sa ran shirin zai kai ga kasashe 14 a yammaci da gabashi da kuma kudancin Afirka.
Kamfanin Facebook zai yi amfani ne da na’urorin tauraron dan Adam da jirgi maras matuki domin baiwa mutane biliyan ‘daya damar shiga yanargizo musammam a yankunan karkara.
Tuni dai wasu kasashe 20 suka fara cin moriyar wannan shiri a wasu sassan duniya.
“Burin Facebook shine ya hada sassan duniya, munyi amanna cewa fasahar tauraron dan Adam za ta taka rawar gani wajen kawar da shingayen da suka raba nahiyar Afirka da sauran kasashen duniya.” In ji mataimakin shugaban kamfanin internet.org Chris Daniels a wata sanarwa da ya fitar.