Lukman Haruna dan wasan kungiyar Super Eagles ya dora laifin rashin tabuka abin kirki da kungiyar ta yi a wasan su da suka yi a Tanzaniya, da cewa rashin kyakykyawan yanayi ne yasa suka kasa tabuka komai a wasan na neman samun guri a gasar cin kogin nahiyar Afirka ta shekara ta 2017.
‘yan wasan Tanzaniya Taifa Stars dai sun tashi kunnen doki da Super Eagle a wasan su na ranar Asabar. Alokacin da Haruna ke magana a jiya Litinin ya tabbatar da cewa rashin kyakykyawan yanayi ne yasa baiyi abin kirki ba, yayi fatan cewa za’a kara bashi dama domin ya nuna bajintar sa.
Anzhi Makhachkala dan wasan da shi ma ya wakilci Najeriya a wasan matasa ‘yan kasa da shekaru 20 wato U-20 dana ‘yan kasa da shekaru 23 wato U-23.
Ya kuma zamanto kaftin a kungiyar Golden Eaglets a wasan da suka buge kasar Spain da ci 3 da babu lokacin da suka buga fanalti a wasan karshe.