Wasu Matasa A Lagos Sunyi Jerin Gwano Domin Nuna Goyon Baya ga Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya

Matasan jihar Lagos, sunyi jerin gwano domin nuna goyon baya ga sojojin Najeriya, a yakin da suke da ‘yan kungiyar Boko Haram.

Matasan da basu kai ashirin da hudu ba, sunyi wannan jerin gwanon ne a ranar Asabar a Lagos, domin nuna goyon bayansu ga sojojin Najeriyar kan yakin da suke da mayakan Boko Haram, a arewa maso gabashin kasar.

Sun dai fara ne daga dandalin Tafawa Balewa, sun kuma ‘dunguma cikin zafin rana har hedikwatar rundunar sojoji ta tamanin da daya, dake unguwar Victoria Island inda jami’an sojojin suka ki magana dasu.

“mun zo nan ne kawai domin tsaro, bamu da ikon karbar wata wasika,” inji wani soja alokacin da yake maida martani ga matasan, wanda suke rokon sa daya karbi wata takardar nuna goyon baya da matasan suka sakawa hannu.

Wadanda suka shirya jerin gwanon dai sunce wannan hanya ce ta nuna goyon baya da girmamawa ga sojojin Najeriya, a yakin da suke da mayakan Boko Haram.

Ms. Agbeje yace, wannan kuma hanya ce ta karfafa wa sojojin gwiwa, bayan da suka rinka fuskantar caccaka daga wurin ‘yan Najeriya.