Wata Amarya ta yi wa Angonta Yankan Rago

Kamfanin dillancin labaran Vanguard ya ruwaito cewa garin kano ya kadu jiya Laraba, yayinda wata amarya, ‘yar shekaru 18 da haihuwa ta yi wa angonta yankan rago a unguwar Darmunawa.

Ita dai matar mai suna Rahma Hussaini, ana zarginta da aikata laifin ne a gidansu bayan wata ‘yar hatsaniya da tashi tsakanin ta da angon nata mai suna Tijjani Basiru dan shekaru 24 da haihuwa.

Malam Isah Alhasan, makwabcinsu Rahma da Tijjani ya fada wa kamfanin na vanguard cewa a jumma’ar da ta gabata ne aka daura masu aure, ya kuma ce bisa ga abinda aka fada masu, auren dole ne akayi wa Rahma.

Alhassan ya kuma fadi cewa wata kururruwa mai razanawa, ce ta janyo hankalinmu su har suka runtuma zuwa gidan makwabtan nasu, inda suka taras da maigidan kwance shame-shame cikin jininsa.

Nan take dai jama’a suka taru aka kai malam Tijjani asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu.

Malam Alhasan ya kuma ce ba tare da bata lokaci ba aka mika amaryar wurin ‘yan sanda inda take tsare yanzu haka.