A karshen makon da ya gabata an sami rudani akan babbar hanyar Ankpa zuwa Anyigba,a jihar Kogi, inda daliban Jami’ar jihar Kogi, suka yi wata zanga zanga, a bisa dalilin kashe wani dalibin makarantarsu da ake zargin wani jami’in hukumar kare haddura na Najeriya, wato Road Safety( FRSC) da aikatawa.
Wani dan gani da ido ya ce takaddama ta faru ne bayan da dalibin ya ki bada cin hancin Naira 100, abunda ya haifar da duka wanda hakan ya kai ga mutuwa.
Bayan da labarin ya isa cikin jami’ar sai duban daliba suka bazama cikin gari suna kone konen tayoyi, daga bisani suka nufi ofishin jami’an Road Safety.
Anga jami’an ‘yan sanda suna kokarin kwantar da tarzoman domin dawo da doka da oda.
Jaridar Vanguard, ta ruwaito cewa an gudu da jami’an da ake zargi da aikata kisan. Wasu dalibai da aka yi hira dasu sun ce zasu ci gaba da tursasawa har sai gaskiya tayi halinta.
An kira Kwamanda hukumar ta Road Safety a jihar ta Kogi, amma bai dauki wayar sa ba kuma an aike masa da sakon kata kwana babu amsa, amma wani jami’in hukumar da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da afkuwar lamari.