Yara Kanana Sun Bayyana Yadda Aka Kashe Iyayensu

Yara 'Yan gudun hijira a makarantar firamare a Damare, Yola 5

Wasu yara ‘yan kasa da shekaru goma sun bayyana wa babban editan Dandali VOA halin da suka shiga, sanadiyar hare haren da ake kaiwa yankunan su, yaran dai yanzu haka suna zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijira dake Damare Yola a jihar Adamawa.

Ibrahim Alfa ya tattauna dasu domin jin abinda ya faru dasu har suka kasance cikin a wannan sansani na ‘yan gudun hijira, wata yarinya mai suna Monday, ta fada masa yadda maharan suka shiga garin nasu suna ta harbe harben bindigogi, da kuma yadda Allah yasa ta kubuta ta shiga cikin daji tana ta tafiya batare da sanin inda ta nufa ba har ta kai ga wani gari inda mutane suka taimaka mata, kwatsam maharan suka kunno kai garin suna harbe harbe, Allah dai ya sake kubutar da wannan yarinya amma har yanzu yarinyar bata san mai ya faru da iyayen ta ba.

Shikuma wani yaro mai suna Samuel daga garin Michika, wanda ya bayyana mawuyacin hakalin da suka shiga shi da ‘dan uwansa, alokacin da maharan suka kai farmaki garin Michika sun dai sami kubuta zuwa garin Mubi, bayan ‘yan kwanaki aka kaiwa garin na Mubi farmaki.

Daya daga cikin yaran ya fadi yadda maharani suka zo gidansu suna buga kofa inda suka harbe mahaifiyar sa, dama kona musu gida duk akan idonsa hakan ya haddasa masa shiga cikin wani hali na mafarke mafarke marasa kyawu.

Abubuwan da suka faru da wadannan yara abin takaicine, inda wasunsu da dama suka bayyana yadda suka ga ‘yan Boko Haram ke kashe mutane ta hanyoyi dayawa wanda suka hada da yanka, harbi harma da kone kone.