Majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar 21 ga watan maris a matsayin ranar dazuka na duniya, domin wayar da kan alumma dangane da muhimmancin kare dazuka da dasa bishiyoyi a ciki da wajen dazuka.
Kamar yadda majalisar dinkin duniyar ke fada sare bishiyoyi ko kona su na taimakawa wajen matsalolin sauyin yanayi da kimanin kaso goma sha biyu zuwa ashirin cikin dari.
Masana ilimin kasa na fadin cewa dazuka kashi ‘daya ne cikin uku na sararin shimfidar duniya, wanda ke da matukar alfanu ga rayuwa. Kimanin mutane biliyan ‘daya da miliyan dari shida ne ke dogaro da dazuka domin harkokin su na yau da kullun, kuma gida ne ga kusan tamanin na cikin dari na dabbobi, tsuntsaye dama bishiyoyi, daji na taimakawa wajen daidaitar iska da ake shaka, kuma yana taimakawa wajen kare yankunan masu danshi wajen zaizayar kasa, da ambaliyar ruwa da kuma kare yankunan dake samar da ruwan sha mai kyau kaso saba’in da biyar cikin dari ga al’ummar duniya.
Taken ranar daji da sauyin yanayi a bana, wanda ke bayanin hanyoyin da za’a kare dazuka da niyyar magance matsalolin sauyin yanayi domin samun mahalli amintacce. Duk da alfanun da dazuka ke dashi ga muhalli da cigaban tallalin arziki, dama taimakawa wajen samar da magunguna yawan sare bishiyoyi na kara saka muhalli cikin wani mawuyacin hali.