WASHINGTON, DC —
Ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Sanata Bala Muhammad Kaura, yace zai yi wuya a iya magance duk ayyukan ta’addanci, amma kuma lallai zasu yi kokarin hakan. Ministan yana magana yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da farautar wadanda suka kitsa harin da ya kashe mutane fiye da 70 a tashar motar Nyanya.
Wata kungiyar matasan arewa ta kalubalanci irin yadda gwamnati take tafiyar da aikin kawo tsaro a arewa maso gabashin kasar. Kungiyar tana magana ne kan sace dalibai mata a makarantar sakandare ta Chibok a Jihar Borno.
Duk da dokar hana fita waje baki daya da aka kafa a Wukarin jihar Taraba, mutanen garin sun ce har yanzu ana kashe kashe. Gwamnati ta kafa wannan doka a bayan rikicin da ya barke a tsakanin Jukun da kabilun Hausawa da Fulani na yankin.

Your browser doesn’t support HTML5