A dandalin mu na yau, shirin Samartaka na wannan makon ya tattauna ne akan yadda yawancin samari suka fi son neman fararen ‘yan mata, haka kuma yawancin ‘yan matan su ma sun fi bada karfin su ga samari farare.
Wasu daga cikin ra’ayoyin da muka ji daga samarin, sun nuna cewa yawancin samari na shi’awar fararen ‘yan mata ne saboda daukar ido. Kamar yadda wani matashi da bai bayyana sunan sa ba ya bayyana mana cewar lallai shi ya fi shi’awar farar mace kuma komi rashin halinta haka zai iya maneji da ita.
Da muka wai waya ta bangaren ‘yan matan kuma, yawanci sun nuna cewar lallai samarin na takura masu musamman ma idan mace fara ce. Sun kara da cewar yawanci lokuta idan farar mace na wucewa kusa da majalisa inda samari ke taruwa, zaka ji suna cewa Allah ya basu farar mace koda mayya ce!.
Kamar yadda wata daga cikin ‘yan matan ta bayyana, ta ce ita tana son farin namiji ne ba don komi ba sai don kawai bukatar samun zuri’a mai kyau.
A cikin samarin da muka sami zantawa da su, daya daga cikin su ne kawai ya ce shi bai damuwa da fararen mata saboda a nasa ra’ayin, yawanci sun a fuskantar kalubale ko da kuwa sun yi aure domin kuwa samarin basa daina damun su.
Daga karshe akwai matsalar canza fata wato blicin da yawancin ‘yan mata bakake ke yi domin neman samu adama da su!
Ku saurari cikakken shirin a dandalinvoa.com
Ku ma ku biyo mu a shafin mu na facebook @ dandalinvoafacebook domin tafka fada mana ra’ayoyin ku.