Magoya bayan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zangar lumana, dauke da kwalaye dakuma ganye inda suka karade manyan titunan fadar jihar Adamawa.
Sun dai yi wannan zanga-zangar lumana ce domin nuna bacin ransu kan abinda suka kira kamun dauki ‘dai ‘dai da jami’an hukumar EFCC ke yiwa wasu kusoshin jam’iyyar a jihar, batun da kuma su kace bazai sa su razana ba.
A cewar wani matashi daga cikin masu yin zinga-zangar, yace dalilin daya sa suke gudanar da wannan gangami shine saboda irin cin fuskar da wulakancin da ake yiwa mutane.
A dai ranar Juma’a ne jami’an hukumar EFCC sukayi awon gaba da daya daga cikin ‘dan takarar kujerar sanata na jam’iyyar kwamanda Abdul’aziz Nyako, dan tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako, yayin da jami’an hukumar ke neman sa ruwa a jallo.
Kungiyoyin da suka shirya wannan zanga-zangar lumana sunce dai babu gudu babu ja da baya, koda kuwa za’a kama daukacin ‘yan takarar jam’iyyar ne.
To sai dai wannan ma na zuwa ne yayin da jihar Adamawan ta sake daukar zafi, game da wani hukunci da ake sa ran yankewa a yau talata a kotun daukaka kara, game da karan da kakakin majalisar dokokin jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya shigar yana ma neman da a maida masa kujerar sa ta mukaddashin gwamnan jihar. Wato a cire gwamnan da kotu ta maido mista Bala Ngilari, batun da ka iya bude sabon rikicin siyasa a jihar.
Yanzu haka dai lokacine ke iya tabbatar da yadda zata kaya, yayin da kuma babban zabe ke karatowa.
Your browser doesn’t support HTML5