A jihar Kaduna wasu malaman addinin musulinci dana krista, sunce wajibi ne ‘yan Najeriya suyi hankali wajen zabar shugabanni a zaben dake tafe.
Bishop Edowu Fearon, yana daya daga cikin wadanda suka jayo hankalin matasa a wani taro da wata kungiyar matasa ta arewacin Najeriya, ACAC ta kira a Kaduna don hada kan mabiya addinai game da zaben dake tafe. Edowu, ya gargadi mutane da cewa Najeriya bata bukatar shugaban kasa bisa ga addini, Najeriya na bukatar shugaba bisa ga adalci, kada ya nuna cewa shi musulmi ne ko shi krista ne, kada mutum ya fito yace yanason ya zama shugaban kasa saboda addinin sa wannan bama bukata.
Sheik dakta Ahmed Abubakar Gumi, na daga cikin malaman da suka fadakar a wannan taro, kuma yace idan har anason cimma nasara to ya zama wajibi ayi hakuri. Yace, “Ai matasa sune wuka sune nama a zaman lafiya, saboda haka tunda matasa ne suka dauki wannan yunkuri insha Allahu za’a ga banbanci.”
Kungiyar ACAC data shirya wannan taro na son cimma burin ganin ta wayar wa matasa kawuna, a cewar Alhaji Aminu Adam daya daga cikin daraktocin wannan kungiya, yace, an kaddamar da wannan kungiya domin ganin an samu zaman lafiya ga al’ummar musulmi da krista a Najeriya.
Saurari cikakken wannan rahoto.