Zauren Matasa: Kan Kudaden Da Kasar Switzerland Zata Mayarwa Najeriya

Dalar Amurka

Wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, shine ya jagoranci tattaunawar Zauren Matasan da ya sami bakuncin Hassan Sardauna mai yaki da cin hanci da rashawa da kuma Hassan Gimba Ahmed Dan siyasa. Inda suka tafka muhawara akan kudaden da aka sace a lokacin mulkin marigari Sani Abacha.

Duk da yake dai wasu ‘yan Najeriya na cewa basu ga abinda akayi da tsabar kudi kimanin dalar Amurka Miliyan 723 (Naira Biliyan 142.43), kudin da Janaral Sani Abacha da kasar Switzerland ta dawowa da Najeriya ba a shekaru goma da suka wuce.

Yan zu haka dai kasar Switzerland na shirin dawowa da Najeriya ragowar kudin, Dala Miliyan 321 (Naira Biliyan 63.24). cikin zauren matasa an tattauna kan tsarin da ya kamata abi alokacin da aka dawo da wadannan kudade, domin tabbatar da cewa anyi wasu ayyuka da talakawa zasu mora.

Kamar yadda akaji a baya an dawo wa da gwamnatin Najeriya da wasu murden kudade, to amma rashin sanin yadda akayi da kudaden na ci gaba da tayarwa da mutane hankali har ma da tsoron cewa kudaden fa na kara salwanta ne, ba tare da talakawa sunci moriyar kudaden ba. Sai dai masu muhawarar na ganin tun da yake an sami sabuwar gwamnati da ake ganin tana kwatanta adalci, wadda kuma talakawa suka amince da ita, da akwai alamar cewa za a gudanar da kudaden ta hanyar da ya kamata.

Saurari Muhawarar cikin sauti.