Zauren Matasa Tare Da Mahmud Ibrahim Kwari

Taron Tattaunawa A Jihar Nasarawa Danagane Da Lafiyar Masu Jego Da Jarirai Da Lafiyar Yara, 21 Agusta 2013

A zaman mahawara na wannna satin zakuji yadda Mahmud Ibrahim Kwari, tare da abokan tattaunawar sa sun ci gaba da mahawara kan sa ido da gutsuri tsoma.

Sa ido nada tasiri kwarai da gaske a cikin gidaje, musamman ‘bagaren zaman zamantakewar aure da mu’amala tsakanin ma’aurata harma da abokan zama, saboda abin na iya kaiwa da kawowa har ma ya kai ga iya illatar da wadanda ake yiwa sa idon, daya daga cikin babbar illar da sa ido ke kawowa itace kiyayya, dalili kuwa shine duk in da akace akwai hassada to kiyayya na biye da ita.

Haka duk wanda ake yiwa sa ido idan ya gano kuma bai kai zuciya nesa ba to shedan na iya raya masa abin kuma yayi ta hayayyafa. Su dai masu wannan halayya ta sa ido, sun kasance mutane ne na kusa bana nesa ba, wannan kuwa na iya kasancewa a cikin gida ko daki daya, ko kuma ma cikin dangi.

A cikin tattaunawar matasan sunyi magana kan abubuwa dayawa daya kamata ace ana sa saka ido akan su domin taimakawa ‘yan uwa wajen cigaban rayuwa, amma sai a buge da sa ido.

Daya daga cikin matasan yayi bayani kan saka ido da kuma sa ido, inda ya bada missalin cewar a kasashen da suka cigaba a duniya su kansu na saka ido domin cigaban kasar su, sai dai inka duba yadda suke saka idon kasan cewa sunayi ne da kyakykyawar manufa. Amma yanzu a kasar hausawa an samu rinjayen sa ido akan saka ido.

Saurari cikkakkiyar tattaunawar matasan.