Jiya talata, majalisar zartaswar hukumar kwallon kafar kasashen Afirka, CAF, ta yanke shawara, ba tare da hamayya ba, kan kawar da ka’idar yawan shekarun duk wani mai son zama jami’in hukumar. Ma’ana, Issa Hayatou zai iya ci gaba da zama a kan kujerar shugabancin CAF wadda ya jima yana zaune daram kanta.
Dukkan wakilai 54 na majalisar suka amince da kawar da dokar da a baya ta ce babu wani jami’in hukumar CAF da zai ci gaba da rike mukaminsa idan ya kai shekara 70 da haihuwa.
Wannan sauyi yazo a garabasa ga Issa Hayatou, wanda yanzu shekarunsa na haihuwa 68 ne, kuma ba zai iya sake neman wannan kujera ba idan wa’adinsa na yanzu ya cika shekarar 2017. Hayatou ya bayyana aniyarsa ta neman sabon wa’adin shekaru 4 zuwa akalla shekarar 2021, a lokacin da zai cika shekaru 75 da haihuwa.
Wannan sabon sauyin dokokin CAF ya biyo bayan nasarorin da ‘yan majalisar zartaswar suka samu cikin ‘yan shekarun nan na daukar matakan dakile tasirin duk masu yin adawa da mulkin Issa Hayatou.