Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daurin Rai Da Rai Akan Laifin Yiwa Yara Kanana Fyede


Kungiyar Lauyoyi mata, ta duniya, ta yi kira ga Gwamnati Najeriya, da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin yiwa yara kanana fyede.

Shugabar kungiyar Mrs. Ngozi Ikenga, ne ta furta haka a wani hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a Abuja a yau talata, tace yakamata a daure duk wanda ya ci zarafin yara kanana tsawon rai da rai.

Tace daukar irin wannan matakin zai sa masu wannan muguwar dabi’a su sake tunani kuma zai kasance ishara ga wasu.

Mrs. Ikenga, ta kara da cewa sau tari yaran da aka yiwa fyade yakan zasu dimuwa wasu kuma yakan bata masu rayuwa ta inda basu iya haihuwa, su kuwa mayan da haka ya faru dasu sukan kasance masu tsanantan maza a rayuwarsu.

Shugaban ta umarci iyaye dasu kai kara ga hukumomin idan har irin haka ya faru ga ‘ya’yan su.

XS
SM
MD
LG