Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dan Kwambo, ya sassauta tsawon dokar ta bacin da aka kafa a ranar asabar din data gabata, daga karfe shida na safe zuwa takwas na dare, jama'a zasu rinka zirga zirga a maimakon na awoyi ashirin da hudu.
idan za'a tuna a ranar asabar din da ta gabata ne kungiyar boko haram ta kaddamar da hare hare a jihar Gomben.
A jiya ne dai mai taimakawa gwamna ta fuskar yada labarai Umar Alkali Jibrin, yayi bayanin sassaucin dokar tabaci, “A takaice dai biyo bayan abinda ya faru, ranar asabar data wuce, gwamnan jihar Gombe mai girma Ibrahim Hassan Dan Kwambo, ya amince da sassauta dokar ta baci daga karfe takwas na yammaci zuwa shida na safiya, ma’ana ana sa ran jama’a zasuyi zirga zirgarsu daga shida na safiya zuwa karfe takwas na yammaci kenan. Shiyasa ake fatan mutane zasu bada cikakken hadin kai da goyon baya musamman ga jami’an tsaro ko masu ayyuka na musamman, ‘yan jarida da masu aikin kwana-kwana, da masu aikin kiwon lafiya da makamantansu wannan doka bata hau kansu ba.”
Mutanen Gombe dai na bayyana jin dadin su game da sassauta wannan doka da gwamnan jihar yayi. A yayin da wasu masu kananan sana’o’i ke kukan cewar ba’a taimaka musu ba kasancewar zasu hada kayansu su tafi gida da karfe takwas tayi.
Sai dai har yanzu babu wani bayani a hukumance kan yawan asarar rayuka, da kuma wadanda suka raunata da dukiyoyi abinda ya fito fili shine an kona wajen ibada da cibiyoyin kula da lafiya dakuma ofisoshin ‘yan sanda.