Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Ya Nuna Ana Samun Karuwar Mashaya Taba Sigari Tsakanin Mata Matasa


Kamar yadda hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya ta tsayar da ranar 31 ga watan Mayun kowacce shekara a matsayin ranar yaki da shan taba sigari ta duniya, mun sami zantawa da wani kwararren likita Dr Issa Ali wanda yayi mana Karin haske akan yadda ake gudanar da wannan yaki da zukar taba sigari da kuma taken yakin na wannan shekarar.

A cewar sa ‘yau ake gudanar da wannan buki na yaki da shan taba sigari, kuma taken wannan shekarar shine yadda za’a rage kayata kwalayen sigari domin rage jan hankalin jama’a masu amfani da ita musammanan matasa.

Wannan ya samo asali tun shekarar 1986 da hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya ta tsayar domin tunawa da wannan rana. Yawancin jama’a kan sami cutar sanakarar huhu, ko ciwon zuciya, har ma da batawa mata masu juna biyu ciki, ko hana mata daukar ciki da ciwon shanyewar jiki da sauran cututtuka da dama duk a sakamakon shan taba sigari.

Ta dalilin haka ne hukumar lafiya ta ga ya kamata duniya baki daya ta yi yaki da wannan abar dake haifar da wandannan cututtuka. Sa’annan idan magidanci na shan taba sigari, bincike ya nuna cewar kusan kashi goma sha biyar cikin dari na adadin kudaden shigar sa kan tafi wajan shan taba sigari ne, dan haka shan taba sigari yana kara talauci a duniya.

Bincike ya bayyana cewa ana samun karuwar masu shan taba sigari musamman a tsakanin mata matasa a kasashe masu tasowa, kuma a cewar likitan wannan babbar matsala ce da ke bukatar a daukar mata mataki domin magance illar da hakan zai iya haifarwa nan gaba.

Ga cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG