Karar da kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Atletico Madrid suka daukaka kan hana su sayen 'yan wasa shekara biyu masu zuwa, ba suyi nasara ba. Kungiyoyin biyu sun kalubalanci hukuncin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, da ta hukunta su, bayan da ta same su da laifin karya ka'idar sayen matasan 'yan kwallo.
Bayan da Fifa ta hukunta kungiyoyin biyu, ta kuma ci tarar Atletico fam 622,000, yayin da Real Madrid za ta biya fam 249,000. Haka kuma hukumar ta ja kunnen kungiyoyin da su guji halin da suka aikata.
A cikin watan Afirilun shekarar 2014, Fifa ta dakatar da Barcelona na tsawon watanni 14 daga sayen 'yan wasan kwallo saboda karya doka wajen sayen 'yan wasan da suke kasa da shekaru 18. Haka kuma an ci tarar kungiyar ta Barcelona fam 305,000.