Wakiliyar sashin Hausa Baraka Bashir ta sami zantawa da wani daga chikin matasa akan yunkurin da suke yi wajan wayar ma sauran matasa kai wato Dalhatu Mohammed musamman yadda zasu fuskanci masu basu kudi domin su kada masu kuri'a.
A cewar Dalhatu Mohammed dai duk dan siyasar da ya ba matshi ko matashiya kudi domin neman kuri'ar su, su amshi kudin amma su san wanda ya kamata su zaba tunda su ke da 'yanci da katunan su babu wanda zaisan wanda suka zaba. "yanzu dai kan mage ya waye" inji wannan matashi.
Daga karshe matashin ya yi kira ga matasa da cewar kar suje wajan zabe da makami ko kuma su nemi tada hankali, talauci na damun mutane amma mutane su san cewa katin su shine 'yancin su. Dan haka kada su sayar amma kudi kam suna iya amsa tunda da ma hakkin su ne.