Lionel Messi ‘dan wasan kungiyar Bercelona ya jefa kwallaye har biyu a raga, yakuma saita wa ‘dan uwansa Neymar kwallo ana saura mintuna 13 wasa ya kare, wasan dai ya karewa Pep Guardiola Koch ‘din kungiyar Bayern Munich da rashin sa’a, inda Bercelona ta lashe wasan daci 3 da babu, a wasan kusa da karshe karo na farko na cin kofin gasar rukunin kwararru na ‘Champion League’.
Karo na 100 a wasan turai Messi ya wuce Cristiano Ronaldo a matsayin wanda yafi kowa jefa kwallaye a wasan rukunin kwararru, yakuma kai kungiyar Bercelona bakin gaba kusa da wasan karshe wannan shine lokaci na farko da suka zo wannan matsayi shekaru hudu da suka wuce.
Manuel Neuer shine ya kokarta wajen baiwa Bayern Munich damar kasancewa a wasan bayan da kare kwallaye har biyar daga shiga raga, amma duk da haka sai da Messi ya jefa kwallon farko a mituna 77 cikin wasa, cikin mintuna yakuma kara wata kwallon.
Messi bai kare haka ba sai da saita wa Neymar kwallo, da haka aka tashi wasa 3 – 0, hakan bai zowa da kungiyar Bayern Munich da sauki ba, a wasan farko da suka fara.
‘yan kallo magoya bayan Barcelona sun karbi Koch din Bayern Munich cikin karramawa, a wannan ziyarar farko da yazo bayan barin tsohon kulub ‘din nasa.