Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Wasu Samari Matasa Akan Tsabatace Jiki Da Amfani Da Kayan Kamshi


Shirin samartaka na dandalin voa a karshen wannan makon ya sami jin ra'ayoyin matasa ne akan tsabtace jiki da amfani da kayan kamshi irin su turare da sauran abubuwa maka mantan su.

Koda shike yawancin samari basu cika amfani da turare ba, domin a cewar su 'yan mata aka sani da amfani da kayan kamshi, wasu daga cikin su sun bayyana cewar hakan ba gaskiya bane domin kuwa a cewar su, masu iya magana sun ce tsabta cikon addini ce.

Akwai abubuwa dama da ya kamata samari su sani agame da amfani da ireiren wadan nan abubuwa, jikin dan'adam a wasu lokuta na bukatar kamshi domin kuwa a cewar wasu daga cikin 'yan matan da muka sami zantawa da su, sun bayyan mana cewar idan wasu mazan suka yi zufa, tsayawa kusa da su kan iya sa mutum amai.

Wasu daga cikin samarin sun bayyana mana yadda basu iya fita ba tare da sun yi wanka da tabbatar da cewar jikinsu baya karni ko wari ba, kuma suna yin hakanne badan neman mata ko son su burge 'yan matan ba.

Saurari cikakken shirin a Danadalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG