Ranar 20 ga watan yuni, ita ce ranar da MDD ta kebe a matsayin ranar ‘yan gudun hijira a duk fadin duniya. Sau tari ana samun ‘yan gudun hijira ne a sakamakon rashin zaman lafiya da yakan addabi wata al’umma ko kuma kuncin rayuwa, kuma yawancin lokuta yara da mata ne suka fi fuskantar wannan hakubar.
Wannan yasa ake kira ga gwamnatocin duniya da suyi hubbasa wajen ganin wannan annoba ta ragu, kuma wadanda suka samu kansu ciki, su sami saukin rayuwa.
Wasu daga cikin abubuwan da hukumar ta MDD mai kula da ‘yan gudun hijirar ke fatar ganin yaran da suka samu kansu cikin wannan halin shine shugabanni su tabbatar sun samu wadataccen ilimi kamar takwarorin su wadanda basu cikin wwannan yanayin rayuwa.
Haka kuma kowane iyali ya samu matsugunni wanda zai tafiyar da rayuwar sa ba tare da tsangwama ba. Haka kuma ko wannne dan gudun hijira ya samu damar koyon wata Sana'a ta yadda zai bada gudunmuwar sa ga al’umma.
Wata kungiyar bada agaji mai zaman kanta tace yanzu haka ‘yan gudun hijira da yawan su yakai dubu 4, fararen hula ne ke zaune a birnin Falluja na kasar Iraqi, wannan ko ya faru tun lokacin da gwamnatin kasar ta kwace yankin Al-Salam. Kuma yanzu haka an mayar dasu a wajen wani sansani dake wajen birnin.
Karl Schembri wani babban jami'in hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway ya shaidawa muryar Amurka daga kasar Bagadaza cewa ko a ranar juma'ar data gabata sai da ‘yan gudun hijira 18 suka mutu, a lokacin da suke kokarin arcewa daga inda ake fada.
Schenbri yace wadannan bayin ALLAH sunyi karo da ajalinsu ne ko biyo bayan kokarin da suka yi na bin hanyar nan da ake cewa tana da saukin wucewa amma basu san cewa an ruruta wannan batu ne bisa karya ba.
Karl Schembri yace sama da yara dubu 20 ne suka samu damar arcewa suka bar kasar, musammam daga lokacin da fadan ya kara kazanta na kokarin ganin an kwace birnin Fallujah a ranar 23 ga watan mayu.
Sai dai kuma a waje daya sojojin sama dake da goyon bayan sojojin Amurka sun kai farmakin a yankin da kungiyar IS take da karfi a arewacin Mosul.
Yanzu haka dai yayin da ake ci gaba da tsabbace mayakan IS a yankin Manjib a Syria, wadanda kuma kurdawa ne ke hakan sai kuma sojojin sakai na Arabia wadanda ‘yan kungiyar Syrian Democratic Forces ne, sa'an nan kuma a waje daya sojojin Libya dake biyayya ga sojojin hadin kan kasar Libya suna kokarin ganin sun kutsa cikin ainihin wurin da kungiyar ta IS ke jin cewa wurinne babbar tunganrta dake Sirte.