Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Matasa Kan Shugabannin Da Basa Aiki


Taron Tattaunawa A Jihar Nasarawa Danagane Da Lafiyar Masu Jego Da Jarirai Da Lafiyar Yara, 21 Agusta 2013
Taron Tattaunawa A Jihar Nasarawa Danagane Da Lafiyar Masu Jego Da Jarirai Da Lafiyar Yara, 21 Agusta 2013

A cikin zauren matasa na yau da wakilin mu Abdulwahab Mohammed ya jagoranta da abokan tattaunawar sa, sun tattauna ne akan batun dokar da ta baiwa talaka damar iya yiwa zababbun wakilai kiranye a mai dasu gida idan sun gaza, ko basa yiwa talakawa ayyukan da suka kamata.

Matakin da za’abi wajen dawo da wakilin da aka zaba wanda baya yiwa talakawa aikin daya dace shine, Zasu iya rubutawa hukumar zabe mai zaman kanta takardar kai, idan aka samu rabin mutanen dake mazabar suka cika takardar kai, suka rubuta sunayensu kuma suka sa hannu cewa suna bukatar hukumar zabe mai zaman kanta da ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin cire wannan wakili. Hukumar zabe zata duba wannan takarda da aka kawo a gabanta, zata kuma tantance idan har tabbas rabin mutanen da sukayi rijistar zabe a wannan mazabar basu amince da wakilinsu ba, to zata gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a idan har mutane kashi hamsin cikin dari suka kada kuri’ar basu yarda da wakilin ba, to hukumar zabe zata rubuta wata takarda zuwa majalisar dokoki ko ta wakilai, daga ranar kuwa shi wannan wakili zai rasa mukamin sa.

Dayawa mutane basu waye da wannan dokar ba, inda ake gani da zarar an zabi wakili ya tafi to koda kuwa baya aikin daya dace mutane basu da yadda zasuyi domin dawo dashi. Wasu kungiyoyin lauyoyi na kokarin fadakar da matasa cikin tarurrukan da suke, da ilimantar da matasa kan wasu tsarirruka da kundin tsarin mulki ya shimfida wanda mutane dayawa basu da masaniya kan dama da ‘yancin ‘yan kasa, suna yin hakane ta hanyar yin jawabi da rarraba wasu katardu ga duk matasan da suka gayyata.

Saurari tattaunawar matasan.

XS
SM
MD
LG