WASHINGTON, DC —
A yau a shirin mu na mata mun sami zantawa da wata matashiya Fidausi Ibrahim Musa wace take yi wa kasa hidima wato (NYSC) tace burin ta, shine ta mai koyar da dalibai a makaranta tare da gudanar da wasu sana'oi.
Fidausi ta ce karatunta bai hanata yin sana’a ba saboda ta kan yi sabulun wanke-wanke da wasu kayan aiki na mata wadanda suka hada da man gashi wanda take yi da man kwakwa, tun kafin ta kammala karatunta na digiri, inda take sayarwa dalibai .
Ta kuma ja hankali mata cewa bayan ilimi yakamata sun kasance masu wata sana’a domin su zamo masu dogaro da kai ta kuma jaddada amfanin yin sana’a masamman ga matasa saboda rashin aikin kan jawo matsaloli da dama.