WASHINGTON, DC —
Wani mutun mai suna Chinedu, ya kashe dansa dan watani uku, a lokacin da shi da matarsa suke fada a garin Owerri, dake jihar Imo, a karshen makon da ya gabata.
Matar ta dauki jaririn ne domin gujewa duka daga mijinta amma sai ya kasance idanusa sun rufe, naushin da ya kaimata sai ya sauka akan jaririn wanda nan take yace ga garinku nan.
Tuni jami’an ‘yan sintiri suka damke shi, a lokacin da yake jawabi Chinedu, yace matar sa taki wanke masa kayan sawan sa ne kuma tana karya kuma baa bin a yarda da ita bane.