Wani lauyan jabu dan shekaru 47, Ayodele Balogun, ya shiga hannun jami’an ‘yan Sanda a jihar Ogun.
Ayodele Balogun, dan garin Otta, a karamar hukumar Ado Odo Otta,dai ya kwashe shekaru goma, yana gudanar da aikin lauya a jihar batare da ilimi ko lasisin yin haka ba.
Shi dai wannan jabun lauya,dubun sa ta cika ne a lokaci da aka yi karan sa cewa ya damfari wani tsabar kudi har dubu dari da arba’in.
Da yake tabbatar da labarin kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Olumuyiwa Adejobi, yace bada jinkiriba za’a gufanar dashi da sauran wadanda suke da alaka da juna a laifuffukan da aka gano suna da hannu a ciki a gaban kotu.
Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Abdulmajid Ali, yace yayi mamakin kasancewar Ayodele na da hannu a wasu laifuffuka da dama kamar yadda bincike ya gano, ya kuma kara jaddada alkwarinsa na kawar da bata gari daga jihar ta Ogun.