An Gurfanar Da Lionel Messi A Gaban Kotu

A yau za’a fara sauraran kara da aka shigar da ake kalubalantar Lionel Messi da mahaifinsa Jorge a bisa zargin rashin biyar kudaden haraji fiye da dala miliyan hudu da dubu dari biyar.

Mahaifin Messi, dai shi ke kula da duk wani alamarin da ya danganci tafiyar da kudaden Messi, kuma ana tuhumarsu ne dagane da harajin shekara 2007 da 2009.

Hukumar harajin kasar Spaniya, tace sun yi amfani kasashen Belize da Uruguay inda suka adana kudade domin gujewa biyan haraji, hukumar na bukatar a saka masu tara mai yawa da yanke masu zama a gidan yari.

Kudaden da ake tuhumar Messi, akan cewa bai biyar haraji akansu ba kudaden ne da ya samu ta hanyar tallace tallace.

Koda yake Messi da mahaifin nasa sun ce su basu aikata wani laifi ba.