Hukumar NYSC Ta Nemi Gwamnatin Jihar Edo Ta Tabbatar Da Tsaron 'Yan Bautar Kasa

Hukumar NYSC ta nemi gwamnatin jihar Edo data tabbatar da samarwa da ‘yan bautar kasa cikakken tsaro a yayin da akasarin su zasu gudanar da ayyukan zaben gwamnan jihar da za’a gudanar a babban birnin jihar ranar litini idan Allah ya kaimu.

Babban Daraktan hukumar Brig, Janar Sule Kazaure ne yayi wannan kira a lokacin da ya ziyarci hukumomin tsaro daban daban a Binin babban birnin jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana cewa shugaban ya kai ziyarci ofishin shalkwatar rundunar ‘yan sandan jihar, da kuma sauran ofisoshi.

Kazaure ya bayyana cewa amfanin da matasan masu bautar kasa wajan gudanar da ayyukan zabe da hukumar zaben Najeriya INEC ta yi, ya taimaka kwarai wajan samun nasarar zaben. Ya kara da cewa hadin gwiwa tsakanin matasan da jami’an tsaro zai taimaka wajan tabbatar da sahihin zabe da kuma bada kariya ga rayukan matasan masu bautar kasa.