Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ghana, Yace Ba Zai Sake Tsayawa Takaraba

Kwesi Nyantakyi, Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ghana

Shugaban hukumar kwallon kafar Ghana ta GFA a takaice Kwesi Nyantakyi, yace ba zai sake shiga takarar shugabancin hukumar ba, idan wa’adinsa ya kare a shekarar 2019.

Kwesi NYantakyi, ya dare kan wannan mukamin ne tun a shekarar 2005, kuma ya yi wa’adi uku. A zaben da ya gabata, shi kadai ya fito a matsayin dan takara babu wanda ya kara da shi.

Sai dai galibin yan kasar Ghana, ne suke nuna kosawarsu da shugaban, kuma suna kira da ya yi murabus, daga wannan mukamin. Biyo bayan gazawar da Ghana, ta yi wurin daukar kofin gasar cin kofin kasashen Afrika, da aka yi a wannan shekarar 2017, da zabensa da aka yi a hukumar FIFA a matsayin jam’in hukumar zantarwar FIFA.

Shiko Nyantakyi yana ganin ya yi iya bakin kokarinsa, don haka yace ba zai sake shiga takarar shugabancin hukumar cikin gidan ba.