Abubuwan Dake Kawo sa Ido ga Matasan Mu

Daga Hagu zuwa Dama: Comrade Danjuma Bello Sarki, Shugaban Matasa na yakin neman zaben gwamna Yero da Bajoga a karkashin tutar jam’iyar PDP a Giwa, jahar Kaduna, da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na Kaduna ta tsakiya: da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na ja.

A cikin wani zaman tattaunawa da wakilinmu Muhmud Kwari ya jagoranta da wasu matasa mata da maza a birnin Kano, sun tattauna ne akan abubuwan dake haddasa sa ido ga matasan mu.

Kamar yadda ake gani zaman majalisa ga matasa shine ke kawo sa ido ga matasan, amma daya daga cikin matasan na ganin cewar jahilci da rashin aikin yi sune ke jawo ire-iren halayyar sa ido ga matasa, domin jahilci na janyo dakilewar tunani inda mutum bazai iya yin tunanin yadda zai iya gina rayuwa ba, rashin aikin yi ko karanci aiki a kasa, wasu matasan nada abinda zasu iya yi amma saboda girman kai da raina aiki sai suki kulawa dashi. Wadannan abubuwa guda biyu a ganin shi wannan matashi sune makasudin sa ido ga matasan mu.

Mutuwar zuciya na daya daga cikin abin da ke damun wasu matasan mu, neman hanyar da za’a yi arziki cikin gaggawa batare da an sha wahala ba. Idan har gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu basu tashi tsaye sun fadakar akan illar mutuwar zuci ba, to kuwa wasu matasan namu zasu zauna ne a majalisa zaman kashe wando da sa ido.

Saurari cikkakiyar tattaunawar matasan.

##caption:Daga Hagu zuwa Dama: Comrade Danjuma Bello Sarki, Shugaban Matasa na yakin neman zaben gwamna Yero da Bajoga a karkashin tutar jam’iyar PDP a Giwa, jahar Kaduna, da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na Kaduna ta tsakiya: da Shugaban Matasan jam’iyar PDP na ja.##