An Fara Muhawara A Taron Majalisar Dinkin Duniya

Yau ne majlisar dinkin duniya ke fara gudanar da wani gagarumin taro a birnin New York na kasar Amurka inda za a tafka muhawara akan dauwamammun muradun raya kasashe na duniya wanda aka fi sani da sustainable developement goals.

Sakataren majalisar dinkin duniya Ban ki Moon ne ya fara jawabin bude taron wanda wannan lokacin shine karo na saba'in da ake gudanar da taron.

Taron ya shafi matasa a cewar wakilin sashin Hausa Na Muryar Amurka Mahmud Lalo, wanda ya kasance a wurin taron kuma ya yi karin bayanin cewar daya daga cikin manayan muradun da aka shata kuma ake so a aiwatar, ya hada da samar da aikin yi. A cewar sa, samar ma da matasa aikin yi domin su zama masu dogaro da kai na da muhimmanci kwarai.

Akwai batun ilimi wanda shima ya shafi matasa ta ko wane bangare, dan haka taron zai tattauna akan yadda za'a bunkasa harkokin ilimi domin samun ingantaccen ilim ba tare da an wahala ba, da kuma samar da daidaito a tsakanin maza da mata.

A kwai kuma sauran abubuwa kamar su kare muhalli da kuma yadda za a kawar da matsalolin sauyin yanayi. taron zai tattauna akan abubuwa goma sha bakwai ne gabaki daya.

Saurari Karin Bayani.