‘Yan ta’adda sun harbi ‘yan wasan Kano Pillars, sun biyar, hakan ya biyo bayan taresu da ‘yan ta’addan suka yi akan hanyarsu ta zuwa Oweri, a jihar Imo, domin buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Heartland na garin Warri.
Wandanda aka harba sun kasance fitattu a ‘yan wasan kungiyar ta Kano, Pillars, wato Gambo Muhammad, Murtala Adamu, Enaji, da Rueben Obanaya da kuma Moses Ekpayi.
Jami’in labarai na kungiyar ta Kano pillars, Rilwanu Malikawa, ya shedawa wakilin muryar Amurka cewa yanzu tilas tasa an dage wannan wasa da za’a yi, saboda abunda ya faru.
Masu kula da al’almuran wasani masamman wadanda ke tsokaci akan yadda Kano pillars, take tafiyarda al’almuranta galibinsu ra’ayinsu y azo daya cewa wannan bat sari ne na fashi da aka sani ba .