Rundunar 'yan Sandan jahar Neja tace tana ajiye da wasu masu yiwa kasa hidima wato NYSC, akan zargin sata inda suka raba wata Anyanwu Obioma, da kayayyaki a shagon ta.
Kakakin rundunar 'yan Sandan jahar ta Neja, ASP Bala Elkana, yace 'yan sintirin dake kula da harabar inda shagon yake suka cafke su kana daga bisani suka mika su ga hukumar 'yan Sanda.
Yace 'yan NYSC, din Dore Shola Frank, Jimoh Sadiq da Oscar Owolabi, ana zargin su ne da shiga shagon Mrs. Anyanwu Obioma, inda suka yiwa matar fashin Naira 150,000.
Kakakin 'yan Sandan ya kara da cewa ana kuma zargin su da satar Laptop, na kimanin Naira 140,000, da katin waya, da ya kai Naira 159,000 da buhun Shinkafa uku, da kudin shi ya kasance Naira 30,000 da Milo na kimanin Naira 15,000.
Tuni aka sanarda da hukumar NYSC, ta jahar ta Neja, kuma 'yan Sanda na ci gaba da bincike In ji Bala Elkana.