Daliban sashen koyon aikin kanikanci na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria sun sami nasarar kera motar da zasu je wata gasar kere-keren da za a yi a Kasar Holand nan da watan Mayun shekarar nan ta 2015. Gasar dai ta sami tallafin kamfanin hakar main a Shell inda suka bawa daliban damar shiga wannan gasa. A shekarar data wuce dama sun yi yunkurin kera ta farko da suka kwashe wajen watannin bakwai.
Sannan kuma a karo na biyun nan da suka kerata a cikin watan daya na Janairu suka kamala a cikin watannin bitu. Sun nuna cewa lokacin da suka fara yi cewa aka yi ba ma zasu iya ba tunda a Nigeria ma ba a kera mota balle a jami’ar Ahmadu Bello, kamar yadda wasu suka dinga kallon abin a farko. Inji wata daliba Aisha Bande Ummu wadda tana cikin tawagar da suka hada wannan motar.
Shima Sadik Yusuf yace shine wanda ya faro wannan al’amari a matsayin rubutun binciken kamala digirin farko amma bayan y agama ya fita sai kuma ya ci gaba da sa hannu a wajen ganin mafarkin wannan binciken ya zama gaskiya. Sun dai sami nasarar tada wannan mota har ta yi tafiya da taoyinta bayan tada injin motar. Kamar yadda suka ce an sami nasara ne ta hanyar gyara kurakuran da suka yi a bayan.
Shima shugaban sahen tsangayar aikin kanikanci Dakta Muhammad Dauda ya kara da cewa sun kera motar ne don zuwa gasar kera motar da zata zama mai nisan zangon gudu bisa shan man fetur kadan. Daliban jami’ar da mutanen gari sun yi ta kururuwar murnar wannan nasara a lokacin da suka fito a cikin motar da niyyar zagayawar gwaji. Ana ta musu kirarin sai ABU sai Najeriya.