Babu Abinda Gwamnatin mahamadou Issoufou Ta Tabuka Ma 'Yan Nijar - 10/4/2014

'Yan adawa a Jamhuriyar Nijar, sun mayar da martani ga ikirarin cewa shugaba Mahamadou Issoufou ya samy nasarar da dukkan gwamnatocin da aka yi a kasar a can baya ba su taba samu ba, kamar yadda shugaban jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya, bazzoum Mouhammad, yayi ikirari.

Kakakin 'yan adawa a Nijar, ya fadawa wakilinmu a Yamai cewa babu wani abinda gwamnati ta tabuka, kuma zance ne kawai maras tushe ikirarin da shi shugaban da kuma mukarrabansa suke yi.

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Abinda Gwamnatin Mahamadou Issoufou Ta Tabuka A Nijar - 0'45"