Basalona Ta Doke Real Madrid Kuma Ita Ce Farko

Luis Suarez na murnar cin kwallon da suka yi wa kulob din Real Madrid kuma su ne farko a yanzu

Kulob din Basalona ya doke Real Madrid da ci 2 – 1 a karawar da sukayi ranara lahadin da ta gabata kuma hakan yazo daidai da lokacin da Javier Mascherano ke ikararin nuna tabatar da cewa tawagar tasu ta kai cikakkiyar tawaga.

Da farkon wasan , Mathieu dan wasan Basalona ne ya fara jefa kwalon a ragar Real Madrid cikin minti na 19 kacal da fara wasan, sai kuma Real Madrid ya maida martani da kwallo guda ta wajan shaharren dan wasan nan wato Ronaldo a cikin mintuna 31 da fara wasan.

Ana cikin fafatawa bayan mintuna 56 sai Suarez dan wasan Basalona ya sake jefa kwallo ta biyu. Yanzu haka dai kulob din Basa ya lashe wasanni bakwai (7) a jere, kuma hakan ya sa kulob din zama na daya da maki 68 a wasannin LA LIGA, shi kuma Real Madrid na matsayin na biyu (2) da maki 64 daidai.

Daga karshe kasancewar Guardiola a kulob din na Basa, ya nuna tasirin sabon salon wasan da ya amince da shi wato bugun bani in baka, kuma hakan ya sa kulob din yayi nasarar mamaye sauran takwarorin sa.