Taya za’ayi mutane su dai na sa ido ko kuma su rage a wannan zamani namu? Tambayar kenan da muka yiwa Dakta Nu’uman Habib, kwararren masanin halayya da tunanin bil Adama na jami’ar Bayero, dake Kano.
Dakta Nu’uman Habib dai yace baza’a iya dai nawa ba sai dai a rage, kuma hakan zai ragu ne idan har mutane suka gano cewar su kansu su waye su, kasancewar wanda ya isa baya bukatar ya sa ido, kuma baya damuwa da halin da mutane ke ciki irin wannan, domin sa ido gazawa ne kuma wanda ya isa baya sa ido, domin baya son ya kalli mutane yaga sun gaza harma ya ji dadi don ganin cewar basu kai shiba.
Karfafa wa’azantarwa da ilimantar wa akai, kasancewar annabi Muhammad (SAW) yace, gulmar mutum kamar cin naman mutum ne wanda ya mutu, to idan malamai suka tashi suka cigaba da wa’azi harma da tunatar mutane akan illar gulma da sa ido to hakan zai taimaka.
Idan kuma akayi rashin sa’a shi wanda ake yin gulmar tasa ko sa idon ya fuskanta, to kuwa yadda ya dauki wadannan mutane zai canza harma yakuma haddasa rashin jituwa tsakanin jama’a. wannan dabi’a dai na bata tarbiya da kuma shafar mutane ba tare da sanin su ba domin dayawa yawancin abin da ake magana akai na sa ido kirkira ce ba gaskiya bane, kuma tunda yake ba gaskiya bane a bayan ido akeyi, mutum bashi da damar ji bare ya kare kansa.
Ga tabakin Daktan.